rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Faransa

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Dubban mutane sun koma zanga-zanga a Faransa

media
Masu zanga-zanga a Faransa AFP

Dubban mutane ne suka gudanar da zanga-zangar nuna kyamar manufofin shugaban kasar Faransa Emmanuel Macron yau a birnin Paris na kasar Faransa.


Rahotanni sun ce duk da dimbin jami’an tsaron da aka jibge da akalla suka kai 2000 musamman a Cibiyar nan da ake kira Central Opera Square, hakan bata hana masu shiga zanga-zangar haduwa domin nuna fushinsu ba.

An kuma bada labarin cewar an yi wasu kananan zanga-zangogi a a biranen Toulouse da Boreaux, amma ta birnin Paris ce ta kasance gagaruma.

‘Yan sanda a birnin Paris sun bayyana yawan wadanda suka halarci zanga-zangar da cewa sun kai dubu 40, amma masu shirya zanga-zangar sun bayyana cewar mambobinsu da suka halarci zanga-zangar sun haura dubu 160.

Shugabannin zanga-zangar dai sun gaya wa magoya bayansu da su yi zanga-zangar cikin halin nuna rashin amincewa da manufofin shugaban kasar kawai, amma matakin da ‘yan sanda suka dauka akansu ne ya haddasa fasa shagunna da karya wasu abubuwa.