rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Tarayyar Turai

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Za’a kafa rundunar tsaro ta musamman a Turai

media
Mambobin kungiyar tarayyar Turai wikimedia

Burtaniya ta goyi bayan tsarin da Faransa ta fito da shi na kokarin kafa rundunar tsaro ta musamman a wani mataki na inganta tsaro a tsakanin kasashen kungiyar tarayyar Turai bayan ficewar ita Birtaniya a kungiyar.


Wannan maganar ta fito ne daga bakin karamin Ministan tsaro na kasar Burtaniya Frederick Curzon wanda ya ce, London na da matukar kwadayin ganin hakan ta kasance.

Dama dai shugaban kasar Faransa Emmanuel Macron ne ya fito da batun kafa wannan rundunar tsaro da za’a rinka kai wa a duk inda matsalar tsaro ta kunno kai a tsakanin kassahen na Kungiyar tarayyar Turai.

A Watan Disamban da ya gabata ne kasashen kungiyar tarayyar turai 25 suka rattaba hannu ga yarjejeniyar samar da tsaro na bai-daya, inda suka bayyana aniyar su ta kafa rundunar hadin guiwa da za ta kula da karfafa tsaro a kasashen yankunan na Turai.

An kuma bayyana cewar duk da cewar kasar Burtaniya ta bayyana daukar matakin ficewarta daga kungiyar, za’a bari ta taka rawa a cikin wannan shirin da ake saboda yadda kasar ta Burtaniya ta bayyana kwadayin ci gaba da kasancewa cikin abubuwan da suka shafi kungiyar tarayyar Turai, koda yake ba zata ci gaba da kasancewa cikin kungiyar ba.