rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Faransa Jamus Birtaniya Iran Amurka Nukiliya

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Kasashen Turai na kokarin shawo kan Trump game da nukiliyar Iran

media
Shugaban Amurka Donald Trump ya sha bayyana yarjejeniyar nukiliyar Iran a matsayin shiririta, abin da ya ce, ba zai amince da shi duk da cewa manyan kasashen duniya sun yi madalla da yrjejeniyar wadda aka kulla a shekarar 2015. NICHOLAS KAMM / AFP

Kasashen Birtaniya da Faransa da Jamus sun kaddamar da wani mataki na karshe wajen shawo kan shugaba Donald Trump na Amurka domin amincewa da yarjejeniyar nukiliyar Iran, in da suke gargadin cewar watsi da yarjejeniyar na iya tinzira samun karuwar makaman.


Ministan Harkokin Wajen Jamus, Heiko Maas ya bayyana cewar muddin Amurka ta yi watsi da yarjejeniyar, to babu shakka yankin Gabas ta Tsakiya na iya fadawa cikin wani sabon tashin hankali, in da yake cewa ya dace Amurka ta fahimci cewar hada kai da Turai zai haifar da zaman lafiya a fadin duniya.

Takwaransa na Faransa, Jean Yves Le Drian da ke ziyara a  Berlin ya ce, ta hanyar yarjejeniyar ce kawai za a hana Iran mallakar makamin nukiliya da kuma raba duniya da barazana.

Shi kuwa Sakataren Harkokin wajen Birtaniya Boris Johnson da yanzu haka ke ziyara a Amurka ya yi gargadin cewa, kuskure ne babba a bijirewa yarjejeniyar wadda aka dauki dogon lokaci kafin shawo kan Iran ta amince da ita.

Ana saran Johnson ya gana da mataimakin shugaban Amurka Mike Pence da Mai bai wa shugaba Trump shawara kan harkokin tsaro, John Bolton da kuma shugabannin kwamitin harkokin wajen Majalisar Amurka domin ganin sun shawon kan Trump wajen kauce wa watsi da yarjejeniyar.