Isa ga babban shafi
Iran-nukiliya

Abubuwan da yarjejeniyar nukiliyar Iran ta kunsa

Yarjejeniya nukiliyar Iran da shugaban Amurka Donald Trump ke shirin fayyace matsayinsa akai wani lokaci a yau Talata, an kwashe tsawon watanni 21 ana tattaunawa akan ta tsakanin Iran da kasashen Birtaniya da China da Faransa da Rasha da Amurka da Jamus da Majalisar Dinkin Duniya da kuma kungiyar kasashen Turai kafin kulla ta.

Wasu ma'aikata tsaye a gaban wata tashar samar da makamin nukiliya a kasar Iran
Wasu ma'aikata tsaye a gaban wata tashar samar da makamin nukiliya a kasar Iran REUTERS/Mehr News Agency/Majid Asgaripour/File Photo
Talla

Manyan batutuwan da ke cikin ta sun hada da rage amfani da Uranium wajen samar da makamashi daga ton 19,000 da kasar ke samarwa zuwa 5,060 nan da shekaru 10 masu zuwa.

Yarjejeniyar ta kuma bayyana rage ton 12 na sinadaren hada makamin nukiliya da Iran ke tarawa zuwa kilo 300 nan da shekaru 15 masu zuwa.

Bangarorin sun kuma amince da sanya hukumar hana yaduwar makamin nukiliya domin kula da aikin da Iran ke gudanarwa a tashoshinta, kuma ya zuwa yanzu jami’an hukumar sun gudanar da bincike har sau 9 ba tare da ganin Iran ta saba yarjejeniyar ba.

Yarjejeniyar ta bada damar cire wa Iran wani sashe na takunkumin da aka dora mata da kuma bude kofofinta ga masu zuba jari wanda tuni manyan kamfanonin Faransa irin su Total da Renault suka kutsa kai.

Ana dakon shugaba Trump ya yanke hukunci kan makomar  wannan yarjejeniya wadda ke neman raba Amurka da kawayen ta na Turai.

Majalisar Dinkin Duniya da kungiyar kasashen kasashen Turai da kuma manyan kawayen Amurka da suka hada da Faransa da Jamus da Birtaniya na ci gaba da kokarin ganin Amurkan ta ci gaba da mutunta wannan yarjejeniya da aka kulla a shekarar 2015.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.