Isa ga babban shafi
Armenia

Shugaban 'yan adawa ya zama Firaminista a Armenia

Majalisar kasar Armenia ta zabi shugaban ‘yan adawar kasar Nikol Pashinyan a matsayin Firaminista bayan share makwanni ana zanga-zangar kyamar jam’iyya mai mulkin kasar.

Nikol Pachinian, sabon Firaministan Armenia
Nikol Pachinian, sabon Firaministan Armenia Sergei GAPON / AFP
Talla

Zaben Pashinyan na zuwa ne bayan da jam’iyya mai mulki ta juyo ga goyon bayan shi a matsayin Firaminista kuma 'yan majalisu 59 ne suka amince, a yayin da 42 suka nuna rashin amincewa.

Kiris ya rage jam'iyyar mai mulkin ta ki amincewa da shi a makon da ya gabata, abin da ya yi wa kasar barazanar kara afkawa cikin tashin hankalin siyasa da ya fi na zanga-zanga.

To sai dai Pashinyan a lokacin zaben nasa, ya tabbatar wa al’ummar kasar cewar aikin farko da zai gudanar, shi ne na samar da daidaitacciyar rayuwa ga al’ummar kasar.

Mai shekaru 42, Pashinyan ya fayyacewa duniya aniyarsa ta ganin kasar ta Armenia ta dare daram bisa tirbar dimokradiyya, da kuma karawa dangantakar da ke tsakaninsu da Rasha karfi.

Dama dai Armenia abokiyar kawancen kasar Rasha ce, kuma shugaban kasar ta Rasha Vladimir Putin ya taya Pashinyan murna tare da yi wa kasar fatan samun zaman lafiya mai dorewa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.