rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Iran Amurka Donald Trump Nukiliya Tarayyar Turai

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Trump zai fayyace matsayinsa akan yarjejeniyar nukiliyar Iran

media
Shugaban Amurka Donald Trump. REUTERS/Lee Jin-man/Pool/File Photo

Yau Talata ake sa ran shugaban Amurka Donald Trump zai sanar da matsayinsa na ficewa daga yarjejeniyar nukiliyar Iran ko kuma cigaba da zama a cikinta.


Trump ya dade yana barazanar ficewa daga cikin yarjejeniyar nukiliyar da aka cimma a shekarar 2015, bisa dalilan cewa yarjejeniyar bata shafi shirin kera manyan makamai masu linzami na Iran ba, da kuma rage tasirin da kasar ke da shi a yakin kasar Syria.

Zalika shugaban na Amurka ya ce akwai bukatar sauya tsarin yarjejeniyar ta 2015, ta yadda zata ta rusa duk wani yunkuri na cigaba da shirin mallakar makaman nukiliya anan gaba, ba kamar yadda yarjejeniyar da ke aiki a yanzu ta nuna dakatar da shirin ta yi ba.

Shugabannin kasashen nahiyar turai sun gargadi Trump da cewa muddin ya janye Amurka daga cikin yarjejeniyar nukiliyar to fa tamkar ya rusa yunkurin da aka dade ana yi ne na kawo karshen shirin nukiliyar ta Iran da ma zaman lafiya a yankin gabas ta tsakiya.

Masu sharhi akan Diflomasiya da masana tsaro sun yi gargadin cewa Iran ka iya maido da shirinta na inganta makamashin Uranium da zai kaita ga mallakar makamakin nukiliya, muddin Amurka ta janye daga yarjejeniyar.

Zalika kasar ta Iran ka iya shiga yake-yaken da ake gwabzawa a kasashen Iraqi, Syria, yemen da Lebanon fiye da yadda take da tasiri acikinsu baya.