Isa ga babban shafi
Iran-Amurka

Kasashen duniya sun mayar da martani kan nukiliyar Iran

Manyan kasashen yammacin duniya sun mayar da martani bayan shugaban Amurka Donald Trump ya sanar da matakinsa na ficewa daga yarjejeniyar nukiliyar Iran, in da suka ce za su ci gaba da mutunta wannan yarjejeniya.

Shugaban Faransa, Emmanuel Macron da Theresa May ta Birtaniya da  Angela Merkel Jamus sun jaddada aniyar ci gaba da mutunta yarjeniyar Iran
Shugaban Faransa, Emmanuel Macron da Theresa May ta Birtaniya da Angela Merkel Jamus sun jaddada aniyar ci gaba da mutunta yarjeniyar Iran REUTERS/Francois Lenoir
Talla

Kasashen Birtaniya da Faransa da Jamus sun ce, za su yi aiki da sauran bangarorin da ke cikin wannan yarjejeniya ta nukiliyar Iran, yayin da suka bukaci Amurka da ta kauce wa haifar da tarnaki wajen aiwatar da yarjejeniyar.

Sauran kasashen da suka rattaba hannu kan yarjejeniyar da aka kulla a shekarar 2015 da suka hada da Rasha da China, su ma sun jaddada aniyar ci gaba da nuna goyon bayansu.

Gwamnatin Iran ta ce, tana aikin ceto wannan yarjejeniya ba tare da Amurka da shugabanta Donald Trump ya sanar da ficewarta ba.

A jiya Talata ne, shugaban Iran Hassan Rouhani ya ce, ya bai wa Ma’aikatar Harkokin Wajen kasar umarnin cimma wata matsaya da kasashen Turai da kuma China da Rasha nan da wasu ‘yan makwanni masu zuwa.

A bangare guda, kasar Japan ta ce, za ta ci gaba da sanya ido kan tasirin ficewar Amurka daga yarjejeniyar, yayin da Firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu ya ce, yana mai cikakken goyon bayan Trump kan matakin da ya dauka.

Ita ma dai Saudiya da ta kasance mai hamayya da Iran ta ce, tana goyon baya da kuma lale marhabin da matakin Trump.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.