rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Iran Isra'ila Amurka Nukiliya

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Isra'ila ta kai wa dakarun Iran hari a Syria

media
Isra'ila ta ce ta dauki matakin kai harin ne bayan ta zargi Iran da fara kai mata a hari a tsaunukan Golan AFP PHOTO/DAVID BUIMOVITCH

Isra’ila ta kai hare-hare da makamai masu linzame a kan sansanonin sojin Iran da ke Syria, bayan da Isra’ilan ta yi zargin cewa wasu rokoki da aka kera a Iran sun fada a yankin tsaunukan Golan cikin daren jiya.


Rahotanni sun ce sojin Syria sun kakkabo wasu daga cikin makaman da Isra’ila ta cilla, yayin da wasu suka fada a kusa da birnin Damascus, to sai dai babu karin bayani a game da irin asarar da wadannan hare-hare suka haifar.

Isra’ilan ta ce, kimanin rokoki 20 dakarun juyin juya halin Iran suka cilla, abin da ta bayyana a matsayin daya daga cikin manyan hare-hare da aka kaddamar mata a cikin gomman shekaru da suka gabata.

Dama dai ana ganin Isra’ila na dakon harin ramako daga Iran tun bayan da dakarun Isra’ila suka hallaka dakarun Iran bakwai a wani hari a Syria a cikin watan Afrilu.

Harin makaman rokan na zuwa bayan shugaban Amurka Donald Trump ya sanar da janyewar kasarsa daga yarjejeniyar nukiliyar Iran.