rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Libya ICC Majalisar Dinkin Duniya Rikicin Kasar Libya

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Kotun ICC na fafutukar cafke wasu kusoshi a Libya

media
Saïf al-Islam Gaddafi, da ga mariya Mu'ammar Gaddafi na Libya na cikin wadanda ICC ke nema MAHMUD TURKIA / AFP

Kotun hukunta manyan laifuka ta duniya, ICC ta bukaci Majalisar Dinkin Duniya ta taimaka ma ta domin cakfe wasu mutane uku da ta ke zargi da aikata laifufukan yaki a Libya, da suka hada da wani baban jami’i na hannun damar Janar Khalifa Haftar da kuma daya daga cikin ‘yayan tsohon shugaban kasar Mu’ammar Gaddafi.


A wata ganawa da wakilan Kwamitin Tsaro na Majalisar Dinkin Duniya, babbar mai shigar da kara Fatou Bensouda, ta ce masu bincike na kotun sun kai ziyara cikin watan Maris da ya gabata a kasar ta Libya, in da suka tattara shaidu da ke tabbatar da cewa mutanen da ake zargin sun aikata laifufukan yaki.

Bensouda ta ce, tuni suka fitar da sammacin kama dan tsohon shugaban kasar Seiful al-Islam Gaddafi, da wani tsohon jami’in tsaron kasar mai suna Al-Tuhamy Mohamed Khaled da kuma wani kwamandan soji Busayf Al-Werfalli.

Kotun dai ta jima tana neman wadannan mutane uku bisa zargin cewa sun taka gagarumar rawa a tashe-tashen hankulan da suka faru kafin da kuma bayan kawar da gwamnatin Mu’ammar Kadhafi a shekara ta 2011.

To sai dai lura da cewa ba wata tsayayyar gwamnati a kasar ta Libya, wannan ya sa Bensouda ke neman goyon Majalisar Dinkin Duniya da kuma Janar Khalifa Haftar da ke rike da muhimman yankunan gabashin kasar domin cafke mutanen.