rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Saudiya Yemen

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Saudiyya ta yi gwajin wata na'urar ankarar da hari

media
Saudiyya dai ta kutsa kai rikicin Yemen ne a shekarar 2015 da nufin hambarar da 'yan tawaye tare da mayar da sahihiyar gwamnati kan mulki. AFP PHOTO/JOSEPH EID

Saudiyya ta yi gwajin wata na'ura da za ta rika ankarar da zuwan hare-hare tare da gano ko an harbo mata makamai masu linzami kasar. Na'urar wadda aka kafa ta a birnin Riyadh yau din nan na zuwa ne kwana guda bayan harbo wasu makamai masu linzami 3 da ake zargin Yemen da harbowa. 


Saudiyyar dai ta gudanar da gwajin na'urar kafin daga bisani ta dasa ta a birnin na Riyadh mai fuskantar hare-hare daga 'yan tawayen Houthi na Yemen, inda kuma ta sanya faifan vidiyon gwajin a shafukanta na tsaro.

A cewar ma'aikatar tsaron kasar, nau'rar za ta taimaka matuka wajen ankarar da al'umma a lokacin da aka harbo wani makami mai hadari ga al'umma.

'Yan tawayen Houthin a Yemen wadanda ke samun goyon bayan Iran a baya-bayan nan suna ta yin luguden makami masu linzami zuwa makociyar kasar Saudiyya wadda ke jagorantar sojin hadakar da ke yaki da su.

Sanarwar da Houthin ta fitar ta tabbatar da harba makaman masu linzami har guda uku inda ta harba biyu zuwa Riyadh daya kuma zuwa Jizan amma kuma sanarwar ma'aikatar tsaron Saudiyya ta ce sun yi nasarar kame dukkanin makaman ba tare da sun illata ko da mutum guda ba.

Saudiyya dai ta kutsa kai rikicin Yemen ne a shekarar 2015 da nufin hambarar da 'yan tawaye tare da mayar da sahihiyar gwamnati kan mulki.

Kawo yanzu dai rikicin ya hallaka akalla mutane dubu 9 da 479 yayin da ya jikkata fiye da mutane dubu 55 a cewar hukumar lafiya ta duniya WHO.

A bangare guda kuma fiye da mutane dubu 2 da dari biyu ne suka mutu a kasar sakamakon amai da gudawa yayinda wasu miliyoyi kuma ke fuskantar tsananin yunwa saboda kawanyar da aka yi musu.