rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Amurka Iran Nukiliya

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Babban jami'in hukumar IAEA ya yi murabus

media
Shalkwatar hukumar IAEA da ke yaki da yaduwar makaman Nukiliya. 路透社

Babban jami’in gudanarwa na hukumar kula da yaduwar makaman kare-dangi a Duniya IAEA da ke karkashin kulawar majalisar dinkin Duniya ya ajiye aikinsa.


Ya zuwayanzu dai ba’a kai ga bayyana dalilin ajiye mukaminsa ba, amma hakan ta faru ne kwanaki kalilan bayan da kasar Amurka ta tsantsame hannuwanta daga yarjejeniyar Nukiliyar Iran.

Hukumar IAEA dai ita ce ta yi aikin tantance ko Iran ta bi dokar hanata ci gaba da sarrafa makamashin Uranium da ake amfani da shi wajen kera makamai masu Linzami.