rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Faransa Rasha Amurka Iran

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Kasashe 5 sun yi watsi da sabon tsari kan yarjejeniyar yanayi ta Paris

media
Jakadiyar Amurka da ke Majalisar Dinkin Duniya Nikki Haley ta soki matakin, inda ta ke cewa Amurka ba za ta bada hadin kai ba. REUTERS/Brian Snyder

Majalisar Dinkin Duniya ta amince da wani tsari da ke gabanta wanda a karon farko zai kai ga samar da karbabbiyar manufa kan muhalli, bisa yarjejeniyar da kasashen duniya suka kulla a taron rage dumamar yanayi ta Paris ta shekarar 2015.


Mafi yawa daga cikin mambobi Kasashe 143 na Majalisar Dinkin Duniya, daga cikin kasashe 193 sun amince da wannan sabon tsari da kasar Faransa ta gabatar.

A bangare guda kuma kasashe 5 ne suka soki tsarin, wadanda suka hada da Rasha, Syria, Turkiya, Philippines da Amurka.

Haka zalika akwai kuma kasashen 7 da suka zama 'yan ba ruwanmu ciki har da kasar Iran sai kuma China da ta goyi bayan matakin.

A watan Satumba ne dai Shugaba Macron na Faransa, ya gabatar da bukatar daukan matakin, wadda zai kasance karon farko ke nan karkashin yarjejeniyar rage dumamar yanayi da kasashen duniya suka kulla a Paris.

Jakadiyar Amurka da ke Majalisar Dinkin Duniya Nikki Haley ta soki matakin, inda ta ke cewa Amurka ba za ta bada hadin kai ba.