rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Rasha Jamus Iran Nukiliya

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Rasha da Jamus sun alkawarta ci gaba da mutunta yarjejeniyar Iran

media
Shugaban kasar Rasha Vladimir Putin. Sputnik/Mikhail Metzel/Pool via REUTERS

Kasashen Jamus da Rasha sun alkawarta ci gaba da mutunta yarjejeniyar nukiliyar Iran duk da ficewar Amurka daga cikin wadda ke a matsayin jagora. kasashen biyu a cewar wata sanarwa da fadar Kremlin ta fitar sun cimma hakan ne yayin tattaunawarsu da juna ta wayar tarho.


A cewar wata sanarwa da fadar Kremlin ta fitar a yau din nan, ta ce tattaunawar tsakanin shugaba Vladimir Putin da takwararsa shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta kai ga cimma matsayar ci gaba da mutunta yarjejeniyar nukiliyar ta Iran duk da ficewar Amurka.

Haka zalika sanarwar ta ce yayin tattaunawar, shugabannin biyu sun kuma tabo halin da ake ciki a Syria a matsayin Rasha na babbar Abokiyar shugaba Bashar al-Assad na Syria.

Tuni dai shugabannin suka tattauna yadda shugabar gwamnatin ta Jamus Angela Merkel ke kokarin kai wata ziyara Rasha a makon gobe.

A makon nan ne dai shugaban Amurka Donald Trump ya yi watsi da bukatun manyan kasashen duniya wajen janye kasarsa daga yarjejeniyar Nukliyar ta Iran wadda aka cimma a shekarar 2015, tare da mayar da wasu takunkuman karya tattalin arziki kan Iran din.

Dama dai shugabar gwamnatin Jamus Angela Merekel ta sanar da matsayar kasar ta cewa za ta ci gaba da mutunta yarjejeniyar inda ta bukaci sauran kasashen Turai da su ci gaba da mara mata baya, a bangare guda shima Putin ya nuna damuwa matuka kan janyewar Amurkan.