rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Iraqi

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

An gudanar da zaben yan Majalisu a Iraqi

media
Nau'rar tanttance masu zabe da aka yi amafani da ita a Iraqi © sami Boukhelifa / RFI

Sama da mutane milyan 24 da dubu dari biyar ne suka samu yin rijista a cewar hukumar zaben kasar Iraki .

Gwamnatin kasar ta baza akala jami’an tsaro da sojoji 900.000 domin sa ido dama tabbatar da tsaro a ilahirin ruhunan zaben kasar.


A watan Fabrairu ne kasar ta Iraki ta samu tallafi na kudi bilyan 30 na dalla domin shirya wannan zabe tareda baiwa hukumomi dake da nauyin shirya zaben damar tattara bayanan da suka dace, to sai dai yan kasar na cigaba da nuna fargaba dangane da ababen da kan iya biyo bayan zaben yan Majalisun kasar.

A karo na farko hukumar zaben kasar Iraqi ta yi amfani da nau'rar zamani dake taimakawa domin tanttance masu zabe .