Isa ga babban shafi
Korea ta Arewa- Amurka

Anya Korea ta Arewa za ta lalata makaman nukiliyarta kuwa?

Korea ta Arewa ba za ta watsar da daukacin makamanta na nukiliya ba kamar yadda wani tsohon mataimakin jakadan kasar a Birtaniya, Thae Yong-ho ya yi hasashe a wata zantawa da manema labarai.

Shugaban Korea ta Arewa Kim Jong-un tare da mukarrabansa a cibiyar gwajin makaman nukiliya
Shugaban Korea ta Arewa Kim Jong-un tare da mukarrabansa a cibiyar gwajin makaman nukiliya KCNA via REUTERS
Talla

Kalaman Yong-ho na zuwa ne gabanin wata ganawa da aka shirya gudanarta tsakanin shugaban Amurka Donald Trump da takwaransa na Korea ta Arewa Kim Jong-un  a ranar 12 ga watan gobe a Singapore.

Yong-ho da wasu masu tunani irin nasa na ganin cewa, Korea ta Arewa za ta yi ha’inci wajen kwance wa kanta makaman nukiliyar da ta mallaka da suka hada da makami mai linzamin da ka iya riskar tsakiyar Amurka da zaran an cilla shi daga kasar.

Tsohon jami’in diflomasiyar ya ce, a karshe Korea ta Arewa za ta kasance mai karfin nukiliya a sirrance, amma kasashen duniya za su rika ma ta kallon wadda ba ta mallaki makamin ba.

Kasar Korea ta Arewa ta sanar wa duniya cewa za ta lalata cibiyar gwajin makaman nukiliyarta a cikin wannan wata na Mayu kuma a gaban kafafen yada labarai na kasasahen duniya da za ta gayyato domin sheda aikin lalata cibiyar, matakin da Trump ya jinjina masa.

Korea ta Arewa ta ce, za ta lalata makaman ne a wani kasaitaccen biki da zai gudana tsakanin ranakun 23-25 na watan da muke ciki.

Wata tattaunawa da Kasar Korea ta Kudu ta jagoranta a bara, ta taka muhimmiyar rawa tsakanin Amurka da Korea ta Arewa har ta kai ga kasashen biyu sun jingine cacar baka a tsakaninsu, in da a yanzu ma aka shirya gudanar da wata ganawa ta musamman tsakanin shugaba Trump da Kim Jong-Un.

Amurka dai na bukatar Korea ta Arewa da ta kwance wa kanta dukkanin makaman nukiliyar da ta mallaka ba tare da sake waiwayarsu ba har abada.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.