rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Iran Tarayyar Turai Amurka Nukiliya

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Iran ta bai wa kasashen Turai wa'adi kan nukiliyarta

media
Jami'an Hukumar Kula da Makamashin Nukiliya ta Duniya sun ce, Iran na mutunta yarjejeniyar da ta kulla da kasashen duniya a shekarar 2015 kan shirinta na nukiliya. KAZEM GHANE / IRNA / AFP

Kasar Iran ta bai wa kasashen Turai kwanaki 60 domin gabatar mata da tabbacin cewar za su mutunta yarjejeniyar nukiliyar da ta kulla da su a shekarar 2015, bayan ficewar Amurka.


Mataimakin Ministan Harkokin Wajen Kasar, Abbas Araghchi ya bayyana haka, yayin da jamiā€™an Iran ke shirin ganawa da wakilan kasashen Faransa da Jamus da Birtaniya a gobe Talata.

Ministan Harkokin Wajen Iran Javad Zarif ya ziyarci China a jiya Lahadi, in da ya gana da hukumomin kasar kafin wucewa zuwa Rasha da kuma Brussels.

Majalisar Dinkin Duniya da Kungiyar Kasashen Turai da kuma kasashen Faransa da Jamus da Birtaniya da suka jagoranci kulla yarjejeniyar, sun ce har yanzu suna tsaye akan ta.

A bangare guda, Sakataren Harkokin Wajen Amurka Mike Pompeo ya ce, a shirye suke su yi aiki da kawayensu na Turai domin daukar matakai kan Iran bayan ficewar kasarsa daga yarjejeniyar nukiliyar.

Pompeo ya ce, a shirye yake ya gabatar da sabbin kudirori domin dakile yadda Iran ke ci gaba da fadada ikonta a Gabas ta Tsakiya.

Sakataren ya ce, nan da 'yan kwanaki ko makonni za su gabatar da sabbin kudirorin da za su yi tasiri kan kasar.