rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Rasha Gasar Cin Kofin Duniya Kwallon Kafa

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Kasashe 32 za su fitar da sunayen 'yan wasan da za su wakilce su a Rasha

media
Kwanaki 31 kadai ya rage a fara gudanar da gasar cin kofin duniyar ta bana wadda Rasha za ta karbi bakwanci, inda za asamu halartar akalla kasashen duniya 32. FIFA.com

A gobe Talata ne kasashe 32 da suka samu gurbi a gasar cin kofin duniya ta 2018 da za ta gudana a Rasha, za su fitar da sunayen ‘yan wasan da za su wakilce su a gasar wadda ta rage kwanaki 31 kadai a fara gudanar da ita.


Sai dai kuma rahotanni na nuni da cewa mafiya yawan kasashen har yanzu na cike da fargaba, musamman ganin yadda wasu daga cikin ‘yan wasansu ke kokarin bijirewa kiranyen da ake kokarin musu don taimakawa kasashensu a gasar ta bana.

A bangaren Argentina, wadda ta zura kwallaye 19 kacal a wasannin 18 na neman gurbin gasar cin kofin duniya ta na bukatar tallafin Giovanni Simeone don taka mata leda a gasar.

Simeone mai shekaru 22 wanda ke taka leda a Club din Fiorentina ana ganin shigarsa gasar zai karawa Lionel Messi kwarin gwiwa wanda shi ya taimaka wajen zura kwallaye 5 da suka bai wa kasar damar samun gurbi a gasar ta cin kofin duniya.

A cewar hukumar kwallon kafar ta Argentina Messi na bukatar mataimaki wanda zai tallafa masa wajen samun karsashin zura kwallaye a gasar.

Baya ga Simeone da ake zawarcin don takawa Argentinar leda a Rashan, akwai kuma ‘yan wasa irinsu Paulo Dybala da Mario Icardi wadanda suma kawo yanzu babu tabbacin ko za su taka leda a gasar.

Ita kuwa hukumar kwallon kafar kasar Crotia ta shidawa FIFA cewa a wannan karon za ta hada tawagar ‘yan wasan da za ta share mata hawaye daga takaicin da ta kunsa a 1998 yayin gasar cin kofin duniya da ta gudana a Faransa.

A cewar kocin kungiyar ta Crotia Zlatko Dalic sai da ya tankade da rairaya tukuna ya zabo tawagar da za ta wakilci kasar a Rasha, wanda a cewarsa ya yi imanin baza su bashi kunya ba.

Dalic ya ce dukkanin ‘yan wasan sun shafe akalla shekaru bibbiyu zuwa uku a tawagar ‘yan wasan kasar, inda y ace za a fitar da sunayensu a gobe Talata .

Iceland ma dai har yanzu tana cike da shakku kan yadda za ta tunkari gasar cin kofin duniyar ta bana a Rasha, la’akari da cewa fitaccen dan wasan kasar da ke taka leda a Everton Gylfi Sigursson har yanzu na fama da jinya.

Tun ranar 3 ga watan Maris ne dai yayin wata fafatawa tsakanin Everton din da Brighton dan wasan gaban Sigurdsson ya samu rauni a kwaurinsa, inda ya kwanta jinya matakin da kociyan kasar ta Iceland hallgrimsson ke cewa babban tashin hankali ne garesu.

Ko da yake dai Club din ya ce dan wasan gaban zai murmure tsakanin makwanni 6 zuwa 8 daga lokacin da ya samu raunin, amma ko a wasan karshe na Everton din jiya lahadi ba’a ga keyar Sigurdsson ba.

A cewar kociyan abu ne mai wuya dan wasan ya iya taka leda a zagayen farko na karawarsu da Argentina a ranar 16 ga watan Yuni a gasar ta cin kofin duniya.