Isa ga babban shafi
Isra'ila-Falesdinawa

An yi jana'izar Falasdinawa 60 da Isra'ila ta kashe

Dubban Al'ummar Musulmi ne yau Talata suka gudanar da jana'izar mutane 60 cikin har da jaririya 'yar watanni 8 da haihuwa da sojin Isra'ila suka hallaka jiya yayin zanga-zangar da Falasdinawan suka yi don nuna adawa da matakin Amurka na mayar da Qudus babban birnin Isra'ilan.

Bayan mayar da birnin na Qudus babban birnin Isra'ila hakan na nufin cewa yanzu yankin na Gaza baya da wani iko da birnin a dai dai lokacin da Isra'ilan ke ci gaba da mamaye yankin na su.
Bayan mayar da birnin na Qudus babban birnin Isra'ila hakan na nufin cewa yanzu yankin na Gaza baya da wani iko da birnin a dai dai lokacin da Isra'ilan ke ci gaba da mamaye yankin na su. REUTERS/Ibraheem Abu Mustafa
Talla

Yayin zanga-zangar ta jiya wadda Falasdinawan ke ci gaba da gunarwa har yau Talata, Sojin na Isra'ila sun yi amfani da makaman gurneti baya ga bindigogi da kuma hayaki mai sanya hawaye wajen tarwatsa su tare da hallaka wasu.

Rahotanni sun ce mutane da dama ne suka fita daga hayyacinsu sakamakon hayaki mai sanya hawayen da Isra'ilan ta yini tana harbawa yankin na Gaza.

Kawo yanzu dai akwai kusan mutane 300 da suka samu mummunan rauni a zanga-zangar ta jiya, ciki har da kananan yara da shekarunsu ya gaza 12.

Tuni dai kasashen Duniya suka yi Allah wadai da matakin yayinda Majalisar Dinkin Duniya ke wani zaman gaggawa kan batun.

Shugaban Turkiyya Recep Tayyib Erdogan ya ce kunnen shegun da Trump ya yi wajen bude ofishin jakadancin kasarsa a birnin na Qudus ya sanya ya rasa ikon fada ajin da kuma martabar da ya ke da ita wajen shiga tsakani don sasanta rikicin gabas ta tsakiya.

Bayan mayar da birnin na Qudus babban birnin Isra'ila hakan na nufin cewa yanzu yankin na Gaza baya da wani iko da birnin a dai dai lokacin da Isra'ilan ke ci gaba da mamaye yankin na su.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.