Isa ga babban shafi
Turai-Iran

Sabon shirin kare yarjejeniyar Nukiliyar Iran daga Turai

Kungiyar kasashen Turai ta kaddamar da wani shirin tattalin arzikin domin cigaba da kare yarjejeniyar nukiliyar Iran bayan ficewar kasar Amurka.

Javad Zarif da shugabar diflomasiyar Turai Frederico Mogherini
Javad Zarif da shugabar diflomasiyar Turai Frederico Mogherini Thierry Monasse/Pool via Reuter
Talla

Bayan ganawar da ministan harkokin wajen kasar Iran Muhammad Javad Zarif da wakilan kungiyar Turai a Brussels, shugabar diflomasiya Frederico Mogherini tace suna daukar matakan ganin Iran ta cigaba da sayar da mai da kuma gas din ta a kasuwannin duniya.

Mogherini tace suna kokarin ganin sun kaucewa takunkumin hada hadar kasuwancin da Amurka ta sanyawa Iran wanda ke aiki a sassan duniya.

Zarif ya bayyana shirin a matsayin matakin farko mai kyau, amma kuma Iran na bukatar tabbatar mata da bukatun da take nema.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.