rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Saudiya Falasdinawa

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Taron kungiyar kasashen Larabawa kan kisan Falesdinawa

media
Shugabanin Kungiyar kasashen Larabawa REUTERS/Hamad I Mohammed

Kasar Saudi Arabia ta kira taron kungiyar kasashen Larabawa gobe alhamis domin tattauna kisan gillar da Israila ta yiwa Falasdinawa sama da 60 ranar litinin.


Kamfanin dillancin labaran MENA yace taron zai baiwa ministocin harkokin wajen kasashen tattauna matakin na Israila da kuma jaddada matsayin su na kin amincewa da matakin Amurka na bude ofishin Jakadancin ta a Birnin Kudus.

Ita ma Turkiya ta kira irin wannan taron, bayan ta kori Jakadan Israila da dake kasar ta, matakin da Israilan ta mayar da martani akai.