Isa ga babban shafi
MDD

MDD ta ce nan da 2050, kashi 68 na al’ummar duniya za su koma a birane

Majalisar dinkin duniya ta yi hasashen nan da shekara ta 2050, kashi 68 na al’ummar duniya za su koma rayuwa a manyan birane. Majalisar ta ce daga cikin mutane biliyan 2 da rabi da zasu kwarara zuwa biranen, kashi 90 na wannan sauyi zai samu ne a nahiyoyin Afrika da Asiya.

Maelfu ya waandamanaji kwenye eneo la Catalonia ambao ni wafuasi wa Puigdemont wakiandamana kupinga kukamatwa kwake nchini Ujerumani. Machi 25, 2018.
Maelfu ya waandamanaji kwenye eneo la Catalonia ambao ni wafuasi wa Puigdemont wakiandamana kupinga kukamatwa kwake nchini Ujerumani. Machi 25, 2018. REUTERS/Albert Gea
Talla

Abinda ya fi daukar hankali a wannan rahoto shi ne yadda ya yi hasashen cewa Nahiyoyin Afrika da Asiya ne ke da kashi 35 daga jimillar kashi 68 na alummar Duniyar da za su kwarara zuwa birane nan da shekaru 30 masu zuwa inda za a samu sauyin a kasashen India, China da Najeriya.

A India mutane miliyan 416 ne za su kwarara zuwa birane, mutane miliyan 255 a China, yayin da a Najeriya nan da shekaru 30 mutane miliyan 189 ne za su yi hijira daga yankunan karkara zuwa birane.

Kididdiga ta nuna cewa yawan al’ummar da ke rayuwa a biranen Duniya ya karu daga miliyan 751 a shekarar 1950, zuwa biliyan 4 da miliyan 200 a shekarar 2018 da muke ciki.

Tokyo shi ne birni mafi yawan al’umma a duniya mai mutane miliyan 37, New Delhi ke biye da shi da mutane miliyan 29, sai kuma birnin Shanghai na uku da mutane miliyan 26.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.