Isa ga babban shafi
Amurka

Harin bindiga ya hallaka dalibai 10 a jihar Texas

Akalla dalibai 10 ne suka rasa rayukansu bayan wani harin bindiga da wani dalibi ya kai kan su a wata babbar makaranta da ke Jihar Texas ta Amurka. Rahotanni sun ce maharin wanda dalibi ne a makarantar ya bude wuta kan 'yan uwansa dalibai ne lokacin da su ke tsaka da hada-hada a safiyar yau Juma'a. 

Ko a watannin baya sai da wani dalibi ya bindige 'yan uwasa dalibai 17 a jihar Florida ta Amurka.
Ko a watannin baya sai da wani dalibi ya bindige 'yan uwasa dalibai 17 a jihar Florida ta Amurka. Reuters
Talla

Tuni dai shugaban kasar Donald Trump ya bayyana harin a matsayin abin takaici yayinda ya aike sakon jaje ga iyalan wadanda abin ya shafa.

Maharin wanda kawo yanzu ba a bayyana sunanshi ko kuma daga inda ya fito ba, bayanai na nuni da cewa dalibin makarantar ne kuma mai karancin shekaru.

Kamfanin dillancin labaran Faransa AFP ya ruwaito cewa adadin mutanen da suka mutun ka iya karuwa amma dukkanninsu dalibai ne a makarantar.

Harbe-harben babu gaira babu dalili dai ba sabon abu ba ne a kasar ta Amurka wadda ta bai wa kowanne mahaluki damar mallakar bindiga don kare kansa, inda ko a baya-bayan nan sai da wani dalibi ya bindige 'yan uwansa dalibai su 17 a wata babbar makaranta da ke jihar Florida.

Dubban dalibai ne dai a watannin baya suka rika gudanar da zanga-zangar bukatar samar da gyara a dokar mallakar bindiga don kare rayukansu, amma kuma kawo yanzu babu wani sabon mataki da kasar ta dauka.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.