rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Majalisar Dinkin Duniya Gaza Falasdinawa Isra'ila

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Majalisar Dinkin Duniya za ta aike da tawagar masu bincike Gaza

media
Ko a ranar litinin din makon nan sai da Isra'ilan ta hallaka akalla Falasdinawa 60 tare da jikkata fiye da dubu biyu. REUTERS/Ibraheem Abu Mustafa

Hukumar kare hakkin bil'adama ta Majalisar Dinkin Duniya a yau Juma'a ta kada kuri'ar amincewa da aika wata tawagar jami'ai na musamman masu bincike kan laifukan yaki don tabbatar da zargin da ake kan Isra'ila na keta haddin Falsdinawa, bayan da ta hallaka fiye da Falasdinawan 60 a litinin din makon nan.


Kudirin wanda ya samu amincewar akalla mambobin kwamitin 29 daga cikin mambobi 45 wanda mambobi biyu suka ki amincewa da shi yayinda 14 kuma suka kauracewa zaman, na da nufin gudanar da bincike kan kisan wanda majalisar ke zargin ya take hakkin bil'adama.

Majalisar ta yi zargin cewa jami'an tsaron na Isra'ila sun yi amfani da karfin makami kan fararen hular Falasdinawan masu zanga-zangar adawa da matakin Amurka na mayar da kudus babban birnin Isra'ila, matakin da ke a matsayin aikata laifukan yaki.

Tun farko dai babbar hukumar kare hakkin bil'adama ta Majlaisar ce ta bukaci kafa kwamiti na musamman don bincikar zargin cin zarafin bil'adama da kuma kashe fararen hula ba bisa ka'ida ba da ake yi kan Isra'ilan tun bayan fara zanga-zangar Falasdinawan a ranar 30 ga watan Maris.

A iya ranar 14 ga watan nan lokacin da Amurka ke bikin bude Ofishinta a birnin Kudus sojin na Isra'ila sun hallaka fiye da Falasdinawa 60 cikin har da jariri mai watanni 8 baya ga jikkata fiye da dubu 2.