rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Amurka Korea ta Arewa Nukiliya

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Ganawar Trump da Kim na da sukurkucewa

media
Shugaba Donald Trump na Amurka da shugaba Kim Jong Un na Korea ta Arewa Fuente: Reuters.

Daya daga cikin manyan jami’an gwamnatin Korea ta Arewa ya yi watsi da kalaman mataimakin shugaban Amurka Mike Pence da ya bayyana da “sakarci”, abin da ke dada haifar da shakku dangane da ganawar da aka shirya gudanarwa tsakanin shugabannin kasashen biyu.


Mataimakin Ministan Harkokin Wajen Korea ta Arewa, Choe Son-hui ya ce, kasar ba za ta bada hakurin neman tattaunawa ba, yayin da kuma ya yi gargadin sake gwajin makamin nukiliya matukar ganawar ta diflomasjiya ta sukurkuce.

Mr. Choe ya caccaki wata hira da aka watsa a kafafen yada labarai a ranar Litinin da ta gabata, in da aka jiyo Pence na gargadin shugaba Kim Jong-un cewa, “babban kuskure ne kokarin wasa da hankalin Trump.”

Mr. Pence ya kuma ce, matukar Korea ta Arewa ta gaza cimma yarjejeniya da Amurka, to za ta tsinci kanta a irin mawuyacin halin da Libya ta shiga bayan ‘yan tawaye tare da goyon bayan Amurka sun kashe shugaba Moammar Gaddafi, shekaru da sallama makamin nukiliyarsa.

Wannan dai na zuwa ne bayan Korea ta Arewa ta yi barazanar janyewa daga tattaunawar da aka shirya tsakanin shugaba Kim da Trump a ranar 12 ga watan gobe a Singapore.

Hakan kuma ya biyo bayan matsin lambar da Amurka ke yi ma ta ne na ganin ta yi watsi da makamanta na nukiliya baki daya.