rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Korea ta Arewa Korea ta Kudu Amurka Nukiliya

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Korea ta Arewa ta lalata cibiyar gwajin nukiliyarta

media
Cibiyar gwajin makamin nukiliyaar Korea ta Arewa ta Punggye-Ri Planet Labs Inc/Reuters

Korea ta Arewa ta lalata cibiya daya tilo ta gwajin makamin nukiliyarta, a wani mataki na kokarin sassauta tashin hankali a yankin.


‘Yan jaridun kasashen duniya da suka halarci cibiyar gwajin nukiliyar ta Punggye-ri da ke yankin arewa maso gabashin kasar, sun ce sun shaida wata gagarumar fashewa a yayin gudanar da aikin lalatawar.

Mahukuntan Korea ta Arewa sun sanar da aniyarsu ta da lalata cibiyar a farkon wannan shekarar, a wani mataki na farfado da kyakkyawar dangantakar diflomasiya tsakanin kasar da makwabciyarta Korea ta Kudu da kuma Amurka.

Sai dai masa kimiya na ganin cewa, tun a cikin watan Satumban bara ne wani sashi na cibiyar ya ruguje bayan wani gwaji da kasar ta gudanar, abin da masana kimiyar ke ganin cewa, tuni cibiyar ta rasa karsashi.