rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Amurka Korea ta Arewa Nukiliya

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Trump ya janye daga tattaunawarsa da Kim Jong-Un

media
Cikin wasikar ta Donald Trump zuwa ga Kim Jong-Un ya ce har yanzu kofa a bude ta ke matukar Korea ta Arewan ta sauya matsayarta game da ganawar mai cike da tarihi wadda a cewarsa za ta amfani duniya baki daya. REUTERS/Kevin Lamarque and Korea Summit Press Pool/File Photos

Shugaban Amurka Donald Trump ya tabbatar da janyewarsa daga tattaunawar sulhun da za ta gudana tsakaninsa da Shugaban Korea ta Arewa Kim Jong-Un wadda aka shirya za ta gudana tsakaninsu a Singapore ranar 12 ga watan Yuni.


Donald Trump wanda ke sanar da hakan a wata wasika da ya aikewa shugaban na Korea ta Arewa Kim Jong-Un, ya ce ya yaba da lokacin da Kim din ya basu a baya amma sakamakon kalaman baya-bayan nan yasa dole ya janye daga tattaunawar don amfaninsu baki daya.

Wasikar ta ci gaba da cewa, Amurka ta yi fatan yiwuwar tattaunawar don samun zaman lafiya wadda tun farko ba ita ta nema ba, amma har yanzu kofa a bude ta ke ga Kim idan abubuwa sun nutsa.

Cikin wasikar ta Shugaba Donald Trump ya ce duk da Kim na barazana da makaman Nukiliya amma ya sani fa suna da makaman da suka fi nashi wanda kuma basa fatan amfani da shi kan kowacce kasa ko wani bil'adama.

Wasikar ta Donald Trump ta karkare da cewa idan har Kim din ya sauya tunani game da ganawar mai cike da tarihi kar ya ji ko dar wajen kira ko kuma aikewa da wasika ga Amurkan cikin sauri za ta mutunta ganawar, yana mai cewa duniya baki daya ta yi asarar damar tattaunawar mai matukar muhimmanci, wadda ya ce tabbas lamari ne mai cike da bacin rai.