Isa ga babban shafi
MDD

Masu amfani da yunwa a matsayin makami za su fuskanci takunkumi- MDD

Majalisar Dinkin Duniya ta yi barazanar sanya takunkumi kan duk wata Gwamnati ko jami’an tsaro ko kuma ‘yan tawaye da suka hana kayakin agaji isa yankunan fararen hula a kasashen da ake fuskantar yake-yake ko tashe-tashen hankula.Matakin Majalisar wanda ke zuwa a dai-dai lokacin da duniya ke fuskantar barazanar yunwa tuni ya samu amincewar wasu kasashen.

Wasu 'yan Sudan ta Kudu a lokacin da ake rabon abinci a yankin da ke fuskantar yake-yake wanda ya haddasa tsananin yunwa.
Wasu 'yan Sudan ta Kudu a lokacin da ake rabon abinci a yankin da ke fuskantar yake-yake wanda ya haddasa tsananin yunwa. RFI / Gaël Grilhot
Talla

Matakin Majalisar wanda kasashen Ivory Coast Netherlands da Sweden suka shigar a sakaye, bai samu goyon bayan Rasha ba, wadda ke fuskantar kiraye-kiraye kan matsa kaimi ga amininta Bashar al-Assad na Syria don ganin ya bada dama ga jami’an jinkai sun isa yankunan ‘yan tawaye.

A cewar Majalisar a dai dai lokacin da rikice-rikice ke kara tsananta a sassan duniya wasu na amfani da Yunwa a matsayin makami don azabtar da wani bangare.

Kididdigar Majalisar dai ta nuna cewa akalla mutane miliyan 74 na fuskantar tsananin yunwa a kasashen da ke fama da yake-yake.

Mataimakin jakadan majalisar dinkin duniyar Lise Gregoire-van Haare ya ce matakin wani ma’auni ne kan yadda Majalisar za ta fara ladabtar da kasashe don kawo karshen amfani da yunwa a matsayin makamin yaki.

Sai dai Rasha wadda ke taka rawa a Yakin Syria wanda daya ne daga wuraren da ake amfani da yunwar a matsayin makami, ta ce tsananin yunwar da duniya ke fuskanta a yanzu bashi da alaka da yake-yake, face yadda kayakin masarufi ke tashin gwauron zabo, da bala’o’I da kuma sauyin yanayi.

Bayaga Syrian akwai kasashe irinsu Yemen da Sudan ta Kudu wadanda majalisar ke zargi da amfani da yunwa a matsayin makamin yaki.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.