An gana tsakanin Shugabanin Koriya ta Arewa da ta Kudu
Kasar Koriya ta Kudu tace shugaba Moon Jae In ya gana da takwaran sa na Arewa Kim Jong Un a iyakar da ta raba kasashen biyu, kwana guda bayan shugaban Amurka Donald Trump yace ana iya cigaba da shirin ganawar su a watan gobe.
Wallafawa ranar:
Fadar shugaba Moon Jae In tace shugabannin biyu sun kwashe sa’oi biyu suna ganawa a tsakanin su a kauyen Panmunjom, inda suka gana a watan jiya suka kuma bayyana aniyar su na kulla dangantaka mai karfi a tsakanin su.
Sanarwar tace shugabannin biyu sun tattauna hanyoyin aiwatar da yarjejeniyoyin da suka amince a Panmunjom da kuma tabbatar da nasarar ganawar da za’ayi tsakanin shugaba Donald Trump da Kim Jong Un a Singapore ranar 12 ga watan gobe.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu