rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Spain Bakin-haure

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Jami'an Spain sun ceto 'yan Afrika sama da 500 a teku

media
Jami'an ruwan Spain sun ceto 'yan ciranin Afrika sama da 500 a teku REUTERS/Hani Amara

Jami’an sojin ruwa na Spain sun ceto ‘yan gudun hijira 532 da suka fito daga yankin gabashin Afrika da ke kokarin tsallakawa zuwa Turai ta hanyar keta tekun Mediterranian.


Jami’an sojin ruwa sun tsamo ‘yan gudun hijrar da ke tafiya a cikin karamin kwale-kwale, in da aka hangosu sun nufin gabashin kasar ta Spaniya jim kadan bayan da aka samu labarin nutsewar wasu kananan jirage 3 saboda rashin kyawon yanayi.

Kasar Spaniya ita ce kasar da ta fi yawan samun ‘yan gudun hijira da ke tsallakawa Turai a kwanan nan, baya ga kasar Girka.

Wata kungiyar kasa da kasa mai kula da halin 'yan gudun hijira ta ce, fiye da ‘yan gudun hijira dubu 22 da 400 ne suka shiga Turai ta hanyar ruwan kasar Spaniya a wannan shekara.

A kwanan nan ma jami’an da ke gadin gabar ruwan kasar Italiya sun ce, a cikin kwanaki 2 an ceto akalla ‘yan gudun hijira 1,500 a tekun Mediterranean a wani aikin ceto da aka gudanar tsakanin sojin ruwan Italiya da wani jirgin ruwa da kungiyoyi masu zaman kansu suka yi haya da kuma jami’an wata hukuma mai sa ido kan yankunan kasashen nahiyar Turai.

Haka ma wata mata ‘yar gudun hijira, ta haifi da namiji a yankin ruwan tekun Meditarranean bayan da aka ceto ta a kokarin tsallakawa zuwa Turai daga kasar Libya.

Jaririn dai shi ne na 36 da aka taba haifa a jirgi yayin da iyayensa ke kokarin tsallaka ruwan a Meditarranian zuwa nahiyar Turai.