Isa ga babban shafi
Amurka-Turai

EU ta lashi takobin mayar da martani ga Trump

Kungiyar Kasashen Turai ta sha alwashin daukar matakin bai daya cikin gaggawa domin mayar da martani kan kudin harajin da shugaban Amurka, Donald Trump ya kakaba wa kasashensu na cinikin karafa da kuma gorar ruwa.

shugaban Faransa Emmanuel Macron da Firaministan Birtaniya Theresa May da kuma Angela Merkel ta Jamus
shugaban Faransa Emmanuel Macron da Firaministan Birtaniya Theresa May da kuma Angela Merkel ta Jamus REUTERS/Francois Lenoir
Talla

Manyan kasashen Turai sun kwashe watanni suna lallamin shugaba Trump wajen ganin ya cire yankinsu daga shirinsa na sanya haraji kan karafa da gorar ruwan da ake kaiwa Amurka, amma abin yaci tura, matakin da ake ganin zai haifar da rikicin kasuwanci tsakanin Amurka da manyan kawayenta.

Cikin fushi shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta bayyana harajin na Amurka a matsayin haramcacce, wanda zai bude kofar mayar da martani mai tsanani.

Shugaban Faransa Emmanuel Macron ya bayyana harajin a matsayin abin da ba za su amince da shi ba, in da yake cewa za su mayar da martani kamar yadda dokokin duniya suka tanada.

Sakatare Janar na kungiyar tattalin arziki na hadin kan Turai, Angel Gurria ya ce, duniya ta fada cikin mawuyacin halin da ya dace ta mayar da martani akai.

Shugaban kungiyar Turai, Jean Claude Juncker ya bayyana Alhamis a matsayin ranar bakin cikin duniya.

Tuni  Turai ta shata martaninta wadanda suka zarce na Amurka da suka kunshi haraji kan giya da kekunan da Amurka ke kerawa da kuma sinadarin hada giyar.

Kungiyar ta ce, matakin na Amurka zai sa ta asarar kusan Dala biliyan 3 da rabi, kuma ita ma za ta dorawa Amurkar abin da ya zarce haka.

Su ma kasashen Canada da Mexico da harajin na Amurka ya shafa sun mayar da nasu martanin daban daban.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.