rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Lafiya WHO

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Mutane miliyan 7 suna mutuwa duk shekara a dalilin taba sigari

media
Hoton taba sigari. REUTERS/Christian Hartmann/Illustration

Hukumar Lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana cewa akwai karancin yekuwar da ake yi wa jama’a kan illar da ke tattare da sigari wajen haifar da cuta ga zuciyar dan adam.


Bayanin na hukumar WHO ya zo ne yayin da duniya ke bikin yaki da dabi’ar shan taba sigari.

Hukumar ta ce koda yake an samu raguwar masu busa sigari sosai daga shekara ta 2000 zuwa yanzu, tayi gargadin cewa har yanzu ana samu wasu sabbin mutane dake rungumar mummunar dabi’ar.

Alkaluman da hukumar ta WHO ta wallafa sun nuna cewa akalla mutane sama da miliyan 7 ke mutuwa kowacce shekara, sakamakon kamuwa da cutar dake da nasaba da busa taba sigari, cikin su harda 890,000 wadanda basa shan tabar, amma kuma suna shakar hayakin ta.