rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Afghanistan NATO/ OTAN

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

NATO za ta aike da karin dakaru 3000 Afghanistan

media
Aikewa da karin dakarun na zuwa ne a dai dai lokacin da gwamnatin kasar ke sanar da tsagaita wuta a yakin da ta ke da mayakan Taliban don gudanar da bukunkuwan Sallah cikin tsanaki. REUTERS/Kacper Pempel

Rundunar tsaron Nato, ta ce za ta tura karin dakaru dubu uku zuwa Afghanistan domin cigaba da bai wa jami’an tsaron kasar horo.Sakataren kungiyar tsaron Jens Stoltenberg, shi ne ya sanar da haka a daidai lokacin da ministocin tsaron kasashen kungiyar ke shirin gudanar da taro a birnin Brussels.


Jens Stoltengerg ya ce tura karin sojojin zuwa Afghanistan ba wai yana nufin cewa kungiyar na goyon bayan cigaba da amfani da karfi domin murkushe mayakan Taliban ba ne, sai dai hakan wata dama ce domin bai wa dakarun kasar cikakken horo da nufin tabbatar da zaman lafiya da tsaron kasar.

A cewar sa wai suna nufin yin amfani da karfin soji ne zai kai ga samar da zaman lafiya a Afghanistan ba, sai dai abin da su ke fata shi ne samar da rundunar tsaro mai karfi da kuma cikakken horo a kasar.

Stoltengerg ya ce idan har aka samu rundunar soji da ta ‘yan sanda masu karfi, hakan zai tilasta wa Taliban zaunawa kan teburin tattaunawa don samar da zaman lafiya a kasar.

Wannan dai na zuwa ne a daidai lokacin da gwamnatin Afghanistan ke sanar da tsagaita wuta a kan mayakan na Taliban daga yanzu har zuwa karshen watan azumin Ramadana.

Gwamnatin ta ce, ta samu goyon bayan Amurka don aiwatar da wannan shiri na tsagaita wuta sai bayan kammala bukukuwan karamar sallah.