rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Amurka

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

An samu yawaitar masu kashe kansu a Amurka

media
Mataimakiyar Daraktan kula da lafiya Anne Schuchat ta ce kisan kai ya zama bala'i ga iyalai da kuma al'ummomi a kasar ta Amurka. REUTERS/Eric Thayer

Hukumomin kula da Lafiyar Amurka sun bayyana cewar an samu karuwar mutanen da ke kashe kan su a kasar da kashi 30 daga shekarar 1999 zuwa yanzu, wanda alkaluma suka nuna cewar sun kai kusan mutane 45,000.


Wani rahoto da hukumar yaki da cututtuka ta kasar ta fitar ya bayyana kisan kai a matsayin babbar matsalar da ake fama da ita a bangaren kula da lafiya a cikin kasashe 44 daga cikin 50 dake fadin Amurka.

Ko a cikin wannan mako saida fitacciyar mai yin jakankunan mata Kate Spade mai shekaru 55 ta kashe kan ta, matsalar da ta janyo hankalin jama’a da dama kan yadda mutane ke kashe kan su.

Mataimakiyar Daraktan kula da lafiya Anne Schuchat ta ce kisan kai ya zama bala’i ga iyalai da kuma al’ummomin Amurka.