rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Somalia Amurka

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Sojan Amurka ya mutu a kasar Somalia

media
Dakarun kasar Amurka a Somalia Kacper Pempel / Reuters

A Somalia daya daga cikin sojan Amurka na rundunar Africom ya rasa ran sa a wani gumurzu da ya wakana a daf da kan iyaka da kasar Kenya a lokacin da Sojan Somalia, Kenya hade da na Amurka suka kai samame a wata maboyar yan kungiyar Al Shebab.


A shekara ta 2011 ne aka kori yan kungiyar Al Shebab daga birnin Mogadiscio, sai dai hakan bai rage musu kafi ba a kokarin su na wargaza zaman gwamnatin kasar dake samu goyan bayan kasashen Duniya.

An dai bayyana cewa hudu daga cikin dakarun Amurka sun samu munanan raunuka, takanas Shugaban Amurka Donald Trump ya aike da wasikar ta’azziya zuwa iyalan siojan da ya rasa ran sa a kasar ta Somalia.