rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Amurka Tarayyar Turai

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Shugaba Trump ya yi watsi da matsayar da aka cimma a taron G7

media
Donald Trump Shugaban Amurka REUTERS/Yves Herman

Shugaban Amurka da ya halarci taron kasashen G7 da kuma ya kama hanya zuwa kasar Singapore inda zai gana da Shugaban kasar Koriya ta Arewa Kim Jong Un, ya bayyana rashin gamsuwar sa da yadda Shugabanin kasashen G7 suka cimma wasu matsaya a taron G 7 a Canada.


Trump ya bayyana cewa babu ta yadda za su iya canza masa manufofin sa .

Shugaban Amurka Donald Trump ya kuma yi barrazanar daukar wasu matakai zuwa kasashen Turai da Canada, Trump ya danganta Firaministan Canada Justin Trudeau da mara gaskiya.

An dai kamala taron ne a dai-dai lokacin da Shugaban Faransa Emmanuel Macron ya bayyana cewa a shekara ta 2019,Faransa za ta karbi bakuncin taron kasashen G7 a garin Biarritz na kasar ta Faransa.

Kasashen na G7 sun dau mataki na ware akala bilyan uku na dala zuwa ilmantar da yara mata musaman yan gudun hijira a Duniya.