Isa ga babban shafi
Afghanistan

Mutane fiye da goma suka mutu a wani harin kunar bakin wake a Afghanistan

A Afghanistan an samu mutuwar mutane 12 yayin da wasu 31 suka samu raunuka bayan da wani dan kunar bakin wake ya tarwatsa kanshi cikin ginin wata ma’aikatar gwamnati a Afghanistan.

Wani harin kunar bakin wake a kasar Afghanistan
Wani harin kunar bakin wake a kasar Afghanistan DR
Talla

Mai magana da yawun ma’aikatar kiwon lafiyar kasar Waheed Majroh, shi ne ya sanar da wadannan alkaluma kwanaki biyu bayan da gwamnatin kasar ta sanar da tsagaita wuta kan ‘yan Taliban har zuwa karshen watan azumin Ramadana.

A cewar yan kungiyar ta Taliban gwmantin kasar na gaban –kanta ne bayan da ta sanar da tsagaita wuta da su,wanda ga baki daya ya sabawa ka’idojin su.

A makon da ya gabata, Rundunar tsaron Nato, ta ce za ta tura karin dakaru dubu uku zuwa Afghanistan domin cigaba da bai wa jami’an tsaron kasar horo.

Sakataren kungiyar tsaron Jens Stoltenberg, shi ne ya sanar da haka a daidai lokacin da ministocin tsaron kasashen kungiyar ke shirin gudanar da taro a birnin Brussels.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.