rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Tarayyar Turai

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Shirin warware matsalar dangantakar tattalin arziki a Turai

media
Waziriyar Jamus Angela Markel tare da wasu wakilan kasashen G7 ke magana da shugaban Amurka Donal Trump Bundesregierung/Jesco Denzel/REUTERS

A batun warware matsalar dangantakar tattalin arziki a Turai kasashen Faransa da Jamus sun matsa kaimin domin samun daidaiton fahimtar juna da kulla alakar tattalin arziki mai dorewa a Nahiyar Turai, musamman lura da matsalar takunkumin da kasar Amurka ke lankaya wa wasu kamfunnan kasashen da ke aiki a kasashen ketare.


Wata majiya daga fadar gwamnatin kasar Faransa ta ce kasashen Faransa da Jamus na can suna kokarin cimma matakin karshe na sauya fasalin tafiyar tattalin aziki da mu’amallar kasashe masu amfani da kudin Euro da ke a yankin Nahiyar Turai.

Wannan ya biyo ne bayan tattaunawar sa’o’I 14 da ministocin kudin kasashen biyu suka gudanar a babban Otal na Marathon da ke a kasar Faransa.

Dama dai a wurin babban taron kasashe masu amfani da kudin Euro da aka gudanar a ran 29 ga watan Yunin wannan shekarar ne, shugaban kasar Faransa Emmanuel Macron ya fito da wata ajanda ta sauya fasalin harkokin Diplomasiyya, tattalin arziki da huldayyar kasashen da ake kira Euro Zone a turance, a yayin da shugabar gwamnatin Jamus Angela Markel ta mara masa baya da dabarun da za’a yi amfani da su.

A jiya ma ministocin harkokin kudaden kassahen biyu wato Bruno Le Maire na Faransa da Olaf Scholz na Jamus sun kwashe akalla sa’o’I 14 zaune wuri daya suna tattaunawa dangane da wannan batun.

To sai dai duk da tsawon sa’o’in da suka kwashe suna tattaunawar ba’a bayyana ko sun kai ga matsaya ta karshe ko kuma a’a ba, amma dai an ce sun samu ci gaba akan inda ake a baya, duk da cewar sun bayyana har yanzu da sauran zangon da za su tafi kamin kai ga matsayar karshe.

Shugaba Macron dai ya yi tsaye akan kokarin sasantawa tsakanin kassahen da kuma kungiyar tarayyar Turai bayan kwashe shekaru suna fama da batun tsuke bakin aljihu da kwararar ‘yan gudun hijira.

Batun yadda kasashen na Turai za su rinka tsaya wa kansu akan harkokin kasa-da-kasa ba tare da jingina ga Amurka ba, na daga cikin shakuwar da suke akai.