A yau ne shugabannin kasashen Amurka da Korea ta Arewa Kim Jung Un da Donald Trupm za su gudanar da tattaunawar keke-da-keke a kasar Singapore.
Wannan ne dai karon farko da shugabannin kasashen biyu za su hadu da juna a tarihi, a batun kwancewa Korea ta Arewa damarar Makaman kare dangi.
To sai dai masana harkokin Siyasar Duniya na ganin da wuya a samu jituwa a tsakanin kasashen biyu ko bayan tattaunawar. Faruk Muhammad Yabo ya tattauna da Professor Khalifa Dikwa na Jami’ar Maiduguri da ke Arewacin Najeriya, ga kuma yanda hirarsu ta kasance.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu