rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Amurka Korea ta Arewa

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Trump zai kawo karshen atisayin Sojan Amurka a Koriya

media
Shugaban Amurka Donald Trump da na Koriya ta Arewa Kim Jong Un a Singapore REUTERS/Jonathan Ernst

Shirin Shugaban Amurka Donald Trump na kawo karshen atisayen sojin hadin gwiwa da Amurka da Koriya ta Kudu keyi ya baiwa manyan jami’an ma’aikatar tsaron kasar mamaki.


Shugaba Donald Trump ya bayyana matakin ne a wani yunkuri na jaddada aniyar sa ta baiwa Koriya ta Arewa karfin gwiwa kan shirin bude wani sabon babi tsakanin dangantakar kasashen biyu.

Rahotanni daga Koriya ta Arewa sun ce shugaba Kim Jong Un ya amince da gayyatar da Trump ya yi masa zuwa Washington nan gaba.

Haka zalika Shugaban kasar Koriya ta Arewa Kim Jong Un ya gayyaci Shugaba Donald Trump zuwa kasar Koriya ta Arewa.