rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Amurka Donald Trump Tattalin Arziki China Diflomasiya

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

China ta maida wa Amurka martani kan takaddamar kasuwanci

media
Tashar sauke kaya ta Qingdao da ke lardin Shandong a gabashin kasar China. AFP

China ta maida martani kan matakin shugaba Donald Trump na kakaba harajin kashi 25 kan kayayyakin da ta ke shigarwa Amurka da darajarsu ta kai dala biliyan 50.


Yayin mai da nata martanin itama China ta dora harajin kashi 25 kan wasu jerin kayayyakin da Amurka ke kai wa cikinta har 659, da suma darajarsu ta kai dala biliyan 50.

Yayin sanar da matakin gwamnatinsa a jiya Juma’a Trump ya yi gargadin cewa muddin China da mayar da martani zai fadada harajin kan kayan da China ke shigarwa Amurkan da darajarsu ta kai dala biliyan 100.

A Waccan lokacin dai Trump ya ce matakin kan China ya zama tilas domin tauna tsakuwa don aya ta ji tsaro kan yadda wasu kasashe ciki har da China, ke satar fasahohin kere-keren su.