rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

WHO

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Masu wasan na'ura na game na gab da haukacewa - WHO

media
An dai gudanar da gwaji kan wasu matasa wanda kuma ya tabbatar da yadda Game din ke illa ga kwakwalwar jama’a, ko da dai wani rahoto ya nuna cewa sai kusan cutar ta samu mutum da akalla shekara guda ake iya ganewa. pixabay

Hukumar lafiya ta duniya WHO ta koka kan yadda wasan na’ura da aka fi sani da Game ke shirin zama babban bala’I ga al’umma. WHO wadda ta alakanta da wasan nau’rar da Cocaine ko kuma caca ta ce game din na taka muhimmiyar rawa wajen haddasa matsala a kwakwalwar jama’a.


Hukumar lafiyar ta duniya WHO ta ce mutanen da wasan nau’rar ko kuma game ya zame musu jiki kan gamu da rashin lafiya idan basu yi ba, ko kuma a lokuta da dama ya zame musu babbar matsala da za ta kai su ga kwanciya a asibiti.

Shekhar Saxena daraktar sashen kula da masu tabin hankali ta WHO ta ce buga wasan na’urar na game na taka muhimmiyar rawa wajen kara yawan masu tabin hankali a duniya baki daya.

Haka zalika mutanen da game din ta zame musu jiki kan rasa bacci yayinda a bangare guda su ke fama da matsalar yawan mantuwa.

Saxena ta ce akwai fiye da mutanen biliyan 2 da rabi da ke doka wasan na’urar amma ta fi cutar da yara masu karancin shekaru wadanda ke iya kauracewa abinci bacci koma karatu don ganin sun kai wani mataki a wasan.

An dai gudanar da gwaji kan wasu matasa wanda kuma ya tabbatar da yadda Game din ke illa ga kwakwalwar jama’a, ko da dai wani rahoto ya nuna cewa sai kusan cutar ta samu mutum da akalla shekara guda ake iya ganewa.