Isa ga babban shafi
Amurka

Trump ya yi barazanar fadada harajin da ya kakabawa kayan China

Shugaba Donald Trump, ya yi barazanar kakaba karin haraji kan kayan da China ke shigar wa Amurka da darajar kudinsu za ta kai dala biliyan 200.

Shugaban Amurka Donald Trump.
Shugaban Amurka Donald Trump. REUTERS/Carlos Barria
Talla

Trump ya ce kowane lokaci karin harajin na kashi 10, zai iya fara aiki, muddin China ba ta janye matakin ramuwar da ta dauka kan Amurkan ba.

Tuni dai kasar China cikin kakkausan harshe, ta soki barazanar ta Donald Trump, tare da shan alawashin za ta maida wa Amurka martani dai dai da irin duk wani mataki da ta dauka kanta.

A makon da ya gabata ne shugaba Trump ya sanar da kakaba harajin kashi 25 akan kayayyakin da kasar China ke shigarwa Amurka, da darajarsu ta kai ta dala biliyan 50, inda ya ce matakin ya zama tilas a dalilin yadda kasar ta China ke satar fasahohin kayayyaki daban daban da Amurka ke kerawa.

Sai dai duk da cewa Trump ya gargadi China da kada ta kuskura da mayar da martani, sa’o’i bayan kakabawa kayan nata haraji, itama China, ta zayyana kayayyakin da Amurka ke kai wa cikinta akalla 659, cikin har da kayan amfanin gona, da kuma motoci, masu darajar dala bliyan 50, wadanda ta kakabawa harajin kashi 25.

Trump dade yana zargin China da yi wa kamfanonin Amurka, ma’aikata da kuma manomanta barazana ta hanyar aikata ha’ainci a alakar kasuwancin da ke tsakaninsu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.