Isa ga babban shafi
Amurka

Amurka ta fice daga cikin hukumar kare hakkin dan Adam ta MDD

Amurka ta fice daga cikin hukumar kare hakkin dan Adam ta majalisar dinkin duniya, saboda zargin cewa hukumar tana nuna fifiko ga wasu kasashe tare da yi wa Isra’ila rashin adalci.

Jakadiyar Amurka a zauren Majalisar Dinkin Duniya Nikki Haley.
Jakadiyar Amurka a zauren Majalisar Dinkin Duniya Nikki Haley. REUTERS/Mike Segar
Talla

Amurka ta ce daukar matakin ficewar ya zama tilas la‘akari da cewa hukumar ta kare hakkin dan adam mai wakilcin kasashe 47, ta dauki tsawon lokaci tana tsangwamar kasar Isra’ila, duk da cewa akwai kasashen da ke tafka laifukan tauye hakkin dan adam da har yanzu bata dauki mataki akansu ba.

Yayin sanar da matakin ga manema labarai, jakadiyar Amurka a zauren majalisar dinkin duniya Nikki Haley, ta yi amfani da kakkausan harshe, wajen sukar kasashen, Rasha, China, Cuba da kuma Masar, bisa rawar da suka taka, wajen dakile yunkurin Amurka na yi wa hukumar ta kare hakkin dan adam din garambawul.

Kafin zuwan wannan lokaci dai, gwamnatin Donald Trump ta dade tana barazanar ficewa daga cikin hukumar kare hakkin dan adam din ta Majalisar dinkin duniya, muddin aka yi gudanar da sauye-sauye ga tsarinta dai dai da bukatar Amurka.

Wannan dai shi ne karo na uku a jere, da Amurka ke ficewa daga cikin wata yarjejeniya ko hukumar da ta kunshi kasashen duniya, bayan da ta fice daga yarjejeniyar rage dumamar yanayi ta birnin Paris, da kuma yarjejeniyar nukiliyar Iran.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.