Isa ga babban shafi
Rasha-Amurka

Trump na gab da ganawa da Putin na Rasha

Fadar gwamnatin Amurka ta White House ta tabbatar da ziyarar mai bai wa shugaban kasar shawara kan harkokin tsaro John Bolton zuwa Rasha a cikin mako mai zuwa don tattaunawa game da yiwuwar ganawar shugaba Donald Trump da takwaransa Vladimir Putin.

Dmitry Peskov ya ce Rasha na sane da cewa dole wata rana wannan ziyara za ta zo.
Dmitry Peskov ya ce Rasha na sane da cewa dole wata rana wannan ziyara za ta zo. Mikhail Metzel/TASS/Host Photo Agency/Pool via REUTERS
Talla

Sanarwar ta ce bayan halartar John Bolton biranen London da Rome a ranakun 25 zuwa 27 na wannan wata don tattaunawa kan sha’anin tsaro, kai tsaye mashawarcin shugaban na Amurka kan sha’anin tsaro zai zarce Rasha don tabbatar da yiwuwar ganawar ta Putin da Trump.

Tun a jiya Alhamis ne Fadar Kremlin ta Rasha ta ce tana tsammanin ziyarar John Bolton a birnin Moscow a wani bangare na shirye-shiryen ganawar shugabannin biyu.

Da yake bayani gaban wani taron manema labarai, sakataren yada labaran fadar ta Kremlin Dmitry Peskov ya ce Rasha na sane da cewa dole wata rana wannan ziyara za ta zo.

Kafin yanzu dai Kremlin ta ce bata da wata masaniya kan yiwuwar ganawar tsakanin Trump da shugaba Vladimir Putin kafin taron kungiyar tsaro ta NATO da zai gudana ranar 11 ga watan Yuli mai zuwa wanda ake tsammanin Donald Trump na Amurka zai halarta.

A ranar 10 ga watan nan, shugaba Vladimir Putin ya ce a shirye ya ke gana da takwaransa na Amurka matukar shima ya shirya kan hakan, inda ya ce amma dole ganawar ta zamo a birnin Vienna na Austria.

Ganawa ta karshe tsakanin shugaba Trump na Amurka da Takwaran sa na Rasha Vladimir Putin ita ce wadda ta gudana a Vietnam cikin watan Nuwamban 2017 yayin taron kungiyar APEC.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.