rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Lafiya Majalisar Dinkin Duniya

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Yau ce ranar yaki da shan miyagun kwayoyi a duniya

media
Matasa da dama a sassan duniya na gurbata rayuwarsu saboda shan miyagun kwayoyi ISSOUF SANOGO / AFP

Yau ce ranar da Majalisar Dinkin Duniya ta ware don yaki da kwankwada da kuma safarar miyagun kwayoyin da ke sanya maye da kuma gurbata tunanin bil’adama.


Bikin na yau na zuwa ne a dai dai lokacin da kasashe masu tasowa ke fama da yadda matasa ke rungumar mummunar dabi’ar shan wiwi da hodar iblis da magungunan da ke jirkita kwakwalarsu.

Tun a ranar 7 ga watan Disamban shekarar 1987 Majalisar Dindin Duniya ta ayyana wannan rana ta 26 ga watan Yuni a matsayin ranar yaki da sha da kuma safarar kwayoyin.

Taken ranar a bana shi ne, "sauraron yara da matasa shi ne mataki na farko wajen taimaka musu samun ci gaba a fannin  kiwon lafiya da kuma samun kariya’’.

A duk shekara ana samun tallafi daga al’umma da kungiyoyi daban-daban a sassan duniya don magance wannan matsala ta shaye-shaye.

A shekarar 2016 majalisar ta gudanar da wani gagarumin taro kan illar kwayoyin, in da daga karshe ta fitar da wani mataki da mambobinta za su dauka wajen yaki da miyagun kwayoyin.