rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Iran India Amurka

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Amurka ta yi barazanar sanya takunkuman Iran su shafi India

media
Shugaban kasar Iran Hassan Rouhani tare da Firaministan India Narendra Modi yayin wata ganawarsu a Hyderabad da ke birnin New Delhi cikin watan Fabarairun 2018. REUTERS/Adnan Abidi

Amurka ta bukaci India ta yi karatun ta nustu game da alakar da ke tsakaninta da Iran, musamman kasancewarta babbar abokiyar cinikayyarta ta bangaren man fetur.Jakadar Amurkan a Majalisar Dinkin Duniya Nikki Haley ta ce kiran na a matsayin gargadi ga Indiyan a dai dai lokacin da Amurkan ke shirye-shiryen kakaba wasu sabbin takunkuman karya tattalain arziki kan duk wata kasa da ta ki yanke hulda da Iran.


Nikki Halley ta yi gargadin cewa sabbin takunkuman Amurkan na karya tattalin arziki da za su fara aiki ranar 4 ga watan Satumba ba za su yi rangwame kan duk wata kasa da ta yi kunnen kashi wajen kin yanke alakar kasuwanci da Iran ba.

India dai kusan ta la’akara da Iran ne wajen sayen galibin man fetur din da ta ke amfani da shi, inda Iran din ke matsayin kasa ta 3 da ke shigar da man fetur mafi yawa kasar ta India na akalla Yuro biliyan 1 da miliyan 25

Akwai dai kakkarfar dangantaka tsakanin India da Iran ko a baya lokacin da ta ke fama da takunkuman kasashe kafin cimma yarjejeniyar nukiliyarta a 2015.

A cewar Nikky Haley abu ne mai matukar wuya Indian ta iya sauya alakarta da Iran dare guda, amma shawara ce a gareta matukar ba ta bukatar takunkuman su shafe ta.

Nikki Haley ta ce za ta yi wata ganawa da Firaminista Narendra Modi na gaba kadan a birnin New Delhi don jan hankalinsa game da muhimmanci yanke huldarsu da Iran.