rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Rasha Amurka Syria Nukiliya

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Putin da Trump za su gana kan rikicin Syria

media
Shugaban Rasha Vladimir Putin da takwaransa na Amurka, Donald Trump Mikhail Klimentyev/Kremlin via REUTERS

Shugaban Rasha Vladimir Putin ya amince da shirin ganawa da takawaransa na Amurka Donald Trump a wata kasa ta dabam, bayan ganawar da suka yi a Moscow da John Bolton, mai bai wa shugaban Amurka shawara kan harkokin tsaro.


Jim kadan bayan kammala ganawar a ranar Laraba a birnin Moscow, Bolton da  Putin, mai bai wa shugaban Rasha shawara kan kasashen ketare, Yury Ushakov, ya ce a yau Alhamis za a bayyana kasar da wannan ganawa mai muhimmanci za ta gudana.

Ushakov ya ce, batutuwan da tattaunawarta Trump da Putin za ta mayar da hankali sun hada da farfado da kyakkyawar diflomasiyya tsakanin Amurka da Rasha, nazari kan yadda za a lalubo bakin zaren warware yakin kasar Syria, sai kuma tattaaunawa kan sanya idanu kan makaman nukiliya domin kare duniya daga barazanar amfani da makaman.

A cewar mashawarcin shugaban na Amurka, John Bolton da shugaba Putin ko kadan ba su tabo batun takunkuman da Amurka ta kakaba wa Rasha a lokutan baya ba.

Alakar diflomasiyya tsakanin Amurka da Rasha ta shafe shekaru da tabarbarewa, bisa dalilan da suka hada da banbancin ra’ayi game da rikicin kasar Syria, mamaye yankin Crimea na kasar Ukraine da Rasha ta yi, sai kuma zargin Rasha da sa hannnu a zaben shugabancin Amurka na shekarar 2016 da Trump ya yi nasara.