rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Syria Lebanon ‘Yan gudun Hijira

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

'Yan gudun hijirar Syria sun fara komawa gida daga Lebanon

media
Wasu 'Yan gudun hijirar Syria yayin ganawarsu da Firaminista David Cameron a sansaninsu da ke kauyen Bekaa na kasar Lebanon. REUTERS

Dubban ‘yan Syria da ke gudun hijira a Lebanon ne suka fara komawa gida yau Alhamis bayan kaddamar da wani shirin mayar da su muhallansu tsakanin gwamnatocin kasashen biyu.


Shirin mayar da ‘yan gudun hijirar ya biyo bayan tsagaitawar yake-yake a wasu daga cikin yankunan kasar ta Syria da kuma yadda hukumomin kasar Lebanon ke ci gaba da matsa kaimi wajen ganin ‘yan gudun hijirar sun bar kasar su.

Majalisar dinkin duniya dai ta ce akwai ‘yan Syrian dubu 36 da ke samun mafaka a sansanin ‘yan gudun hijira na Arsal a kasar ta Lebanon galibinsu wadanda suka fito daga kauyukan da ke kan iyakokin kasashen biyu.

Kamfanin dillacin labaran Lebanon LNNA ya ce akwai ‘yan gudun hijira 370 da yanzu haka suka bar sansanin na Arsal tare da tsallakawa Syria.

An dai ga tarin mata da kananan yara cikin murna a Wadi Hameid da ke wajen Arsal na hawa manyan motoci a safiyar yau alhamis don mayar da su kasarsu.

Rahotanni sun ce an makare manyan motoci da kayakin ‘yan gudun hijirar, yayinda ake duba takaddun shaidarsu don tabbatar da cewa suna cikin sahun farko na wadanda za a mayar gida.

Babban hafson tsaron kasar ta Lebanon Abbas Ibrahim ya ce jigilar ita ce ta farko karkashin yarjejeniyar da suka kulla da Syrian.

A cewarsa sun gabatarwa Syrian akalla sunayen ‘yan gudun hira dubu 3 da su ke bukatar komawa gida amma 450 ne kadai suka samu sahalewa.