rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Mexico Amurka Donald Trump

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Obrador ya lashe zaben shugabancin Mexico

media
Zababben shugaban Mexico Andre Manuel Lopez Obrador ®REUTERS/Edgard Garrido

Andres Manuel Lopez Obrador, ya lashe zaben shugabancin kasar Mexico da aka gudanar a ranar lahadi kamar dai yadda alkalumman zaben ke nunanawa.


Shugaban Hukumar Zaben Kasar Lorenzo Cordova, a wata sanarwa da ya fitar a safiyar yau, ya ce Lopez Obrador wanda ya fito daga jam’iyyar adawa, ya samu kuri’un da yawansu ya haura kashi 53% a gaban babban abokin hamayyarsa na jam’iyyar masu ra’ayin rikau Ricardo Anaya, wanda ya samu kashi 22%, sai kuma wani dan takarar mai suna José Antonio Meade wanda ya tashi da kashi 16%.

Lopez da ake kira AMLO, a lokacin yaken neman zabensa ya yi alkawarin samar da sauyi a kasar ta Mexico musamman ta hanyar yaki da talauci, rashawa da kuma aikata miyagun laifufuka matukar dai aka zabe shi.

Sabon shugaban shekarunsa 64 a duniya, kuma zai mulki kasar a tsawon wa’adin shekaru 6 masu zuwa. A Lokacin yakin neman zabe, an hallaka ‘yan takawa da kuma manyan ‘yan siyasa akalla 150.

Shi ma dai shugaban Amurka Donald Trump, ya ce a shirye yake domin yin aiki da duk wanda ‘yan kasar ta Mexico suka zaba domin tunkarar matsalar kwarar baki da kungiyoyin masu aikata miyagun laifufuka kan iyakar kasar da Amurka.