rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Majalisar Dinkin Duniya Syria

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

MDD na ci gaba da yin matsi ga Rasha kan hare-haren yankin Deera na Syria

media
haakin da ya turnike a yankin dake rike ga yan tawaye a Deraa, kenan sakamakon lugguden wutar da dakarun syria suka yi a 5 yulin 2018. Mohamad ABAZEED / AFP

Majalisar Dinkin Duniya na cigaba da yin matsin lamba kan Rasha, domin ta samar da hanyoyin bada agaji a kudancin Syria, wacce ke fuskantar lugudan wuta daga dakarun gwamnatin shugaba Bashar Al-Assad.

Sai dai Rasha ta hau kujerar naki kan samar da wani kudirin halin da ake ciki, bayan wani zaman taro da kwamitin sulhun ya gudanar a jiya.


Bayan kamala zaman taron kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya, Jakadan kasar Rasha Vassily Nebenzia ya ce babu wani jawabin bayan taro da kwamitin zai gabatar, sakamakon taron da kasashen Kuwait da Sweden suka kira.

Nebenzia ya ce, suna mayar da hankali ne kan yaki da ta’addancin dake gudana a kudancin Syria, inda yan ta’adda dake dauke da makamai suka samu wurin zama.

Jakadan Swedin a Majalisar Olof Skoog, ya bukaci takwaransa na Rasha da ya taimaka wajen ganin an baiwa tawagar motocin dake dauke da kayan agaji damar kai su ga mabukata a kudanci Siriya, inda yan tawaye suke zafafa lugudan wuta,

Hakan ya biyo bayan sanarwar da Sakatare Janar na MDD ya fitar game da munanan hare haren da ake kaiwa a kudancin Siriya ne, wadanda suka fara a ranar 19 ga watan Yuni, wanda kuma ke da mumunar illa ga fararen hula"

Akalla sama da rayuwakan mutane dubu 750,000 ne ke ciki hatsari, kana sama da mutane dubu 320,000 su ka rasa matsugunansu, abinda ya sa Antonio Gutteres ya jaddada bukatarsa ta neman agaji ba tare da bata lokaci ba